0
stringlengths 3
620
| 1
stringlengths 4
423
|
---|---|
In the dream God responded, “Yes, I know you are innocent. That’s why I kept you from sinning against me, and why I did not let you touch her. | Sai Allah ya ce masa a cikin mafarki “I, na san ka yi wannan da kyakkyawan nufi, saboda haka ne na kiyaye ka daga yin mini zunubi. Shi ya sa ban bar ka ka taɓa ta ba. |
Now return the woman to her husband, and he will pray for you, for he is a prophet. Then you will live. But if you don’t return her to him, you can be sure that you and all your people will die.” | Yanzu ka komar da matar mutumin, gama shi annabi ne, zai kuma yi maka addu’a, za ka kuwa rayu. In ba ka komar da ita ba fa, ka sani tabbatacce kai da dukan abin da yake naka za ku mutu.” |
Abimelech got up early the next morning and quickly called all his servants together. When he told them what had happened, his men were terrified. | Kashegari da sassafe, sai Abimelek ya tara dukan fadawansa, ya faɗa musu duk abin da ya faru, suka ji tsoro ƙwarai da gaske. |
Then Abimelech called for Abraham. “What have you done to us?” he demanded. “What crime have I committed that deserves treatment like this, making me and my kingdom guilty of this great sin? No one should ever do what you have done! | Sa’an nan Abimelek ya kira Ibrahim ciki ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ta wace hanya ce na yi maka laifi har da ka kawo irin wannan babban laifi a kaina da kuma masarautata? Ka yi mini abubuwan da bai kamata a yi ba.” |
Whatever possessed you to do such a thing?” | Abimelek ya kuma ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan?” |
Abraham replied, “I thought, ‘This is a godless place. They will want my wife and will kill me to get her.’ | Ibrahim ya ce, “Na ce a raina, ‘Tabbatacce babu tsoron Allah a wannan wuri, za su kuwa kashe ni saboda matata.’ |
And she really is my sister, for we both have the same father, but different mothers. And I married her. | Ban da haka, tabbatacce ita ’yar’uwata ce, ’yar mahaifina, ko da yake ba daga uwata ba, ta kuma zama matata. |
When God called me to leave my father’s home and to travel from place to place, I told her, ‘Do me a favor. Wherever we go, tell the people that I am your brother.’” | Sa’ad da Allah ya sa na tashi daga gidan mahaifina na ce mata, ‘Wannan shi ne yadda za ki nuna mini ƙaunarki. Duk inda muka tafi, ki ce game da ni, “Shi ɗan’uwana ne.” ’ ” |
Then Abimelech took some of his sheep and goats, cattle, and male and female servants, and he presented them to Abraham. He also returned his wife, Sarah, to him. | Sai Abimelek ya kawo awaki da shanu da bayi maza da mata, ya ba wa Ibrahim, ya kuma komar da Saratu matarsa gare shi. |
Then Abimelech said, “Look over my land and choose any place where you would like to live.” | Abimelek ya kuma ce, “Ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda kake so.” |
And he said to Sarah, “Look, I am giving your ‘brother’ 1,000 pieces of silver in the presence of all these witnesses. This is to compensate you for any wrong I may have done to you. This will settle any claim against me, and your reputation is cleared.” | Ga Saratu kuwa ya ce, “Ina ba wa ɗan’uwanki shekel dubu na azurfa, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa cewa ba ki da laifi.” |
Then Abraham prayed to God, and God healed Abimelech, his wife, and his female servants, so they could have children. | Sai Ibrahim ya yi addu’a ga Allah, Allah kuma ya warkar da Abimelek, da matarsa da bayinsa mata domin su haihu, |
For the Lord had caused all the women to be infertile because of what happened with Abraham’s wife, Sarah. | gama Ubangiji ya rufe kowace mahaifa a gidan Abimelek saboda Saratu, matar Ibrahim. |
The Lord kept his word and did for Sarah exactly what he had promised. | Ana nan sai Ubangiji ya nuna wa Saratu alheri kamar yadda ya ce, Ubangiji kuma ya yi wa Saratu abin da ya yi alkawari. |
She became pregnant, and she gave birth to a son for Abraham in his old age. This happened at just the time God had said it would. | Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari. |
And Abraham named their son Isaac. | Ibrahim ya sa wa ɗan da Saratu ta haifa masa suna Ishaku. |
Eight days after Isaac was born, Abraham circumcised him as God had commanded. | Sa’ad da ɗansa Ishaku ya kai kwana takwas da haihuwa, sai Ibrahim ya yi masa kaciya, kamar yadda Allah ya umarce shi. |
Abraham was 100 years old when Isaac was born. | Ibrahim yana da shekara ɗari, sa’ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku. |
And Sarah declared, “God has brought me laughter. All who hear about this will laugh with me. | Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, kuma duk wanda ya ji game da wannan, zai yi dariya tare da ni.” |
Who would have said to Abraham that Sarah would nurse a baby? Yet I have given Abraham a son in his old age!” | Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.” |
When Isaac grew up and was about to be weaned, Abraham prepared a huge feast to celebrate the occasion. | Yaron ya yi girma, aka kuma yaye shi, a ranar da aka yaye shi kuwa, Ibrahim ya yi babban biki. |
But Sarah saw Ishmael—the son of Abraham and her Egyptian servant Hagar—making fun of her son, Isaac. | Amma Saratu ta ga cewa yaron da Hagar, mutuniyar Masar ta haifa wa Ibrahim yana wa ɗanta Ishaku gori, |
So she turned to Abraham and demanded, “Get rid of that slave woman and her son. He is not going to share the inheritance with my son, Isaac. I won’t have it!” | sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori baiwan nan tare da ɗanta, saboda ɗan baiwan nan ba zai taɓa raba gādo da ɗana Ishaku ba.” |
This upset Abraham very much because Ishmael was his son. | Al’amarin ya ɓata wa Ibrahim rai sosai domin zancen ya shafi ɗansa. |
But God told Abraham, “Do not be upset over the boy and your servant. Do whatever Sarah tells you, for Isaac is the son through whom your descendants will be counted. | Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada hankalinka yă tashi game da yaron nan da kuma baiwarka. Ka saurari duk abin da Saratu ta faɗa maka, saboda ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka. |
But I will also make a nation of the descendants of Hagar’s son because he is your son, too.” | Zan ba ɗan baiwan nan al’umma shi ma, domin shi zuriyarka ne.” |
So Abraham got up early the next morning, prepared food and a container of water, and strapped them on Hagar’s shoulders. Then he sent her away with their son, and she wandered aimlessly in the wilderness of Beersheba. | Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba. |
When the water was gone, she put the boy in the shade of a bush. | Sa’ad da ruwan da yake cikin salkan ya ƙare, sai ta ajiye yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace. |
Then she went and sat down by herself about a hundred yards away. “I don’t want to watch the boy die,” she said, as she burst into tears. | Sai ta tafi, ta zauna ɗan nesa da yaron, misalin nisan harbin baka, gama ta yi tunani ta ce, “Ba zan iya kallon yaron yana mutuwa ba.” Da ta zauna nesa da yaron, sai ta fara kuka. |
But God heard the boy crying, and the angel of God called to Hagar from heaven, “Hagar, what’s wrong? Do not be afraid! God has heard the boy crying as he lies there. | Allah kuwa ya ji yaron yana kuka, sai mala’ikan Allah ya kira Hagar daga sama ya ce mata, “Mene ne damuwarki, Hagar? Kada ki ji tsoro, Allah ya ji yaron yana kuka yayinda yake kwance a can. |
Go to him and comfort him, for I will make a great nation from his descendants.” | Ki ɗaga yaron ki riƙe shi a hannu, gama zan mai da shi al’umma mai girma.” |
Then God opened Hagar’s eyes, and she saw a well full of water. She quickly filled her water container and gave the boy a drink. | Sa’an nan Allah ya buɗe idanunta ta ga wata rijiyar ruwa. Don haka sai ta tafi ta cika salkan da ruwa, ta kuma ba wa yaron ruwa ya sha. |
And God was with the boy as he grew up in the wilderness. He became a skillful archer, | Allah ya kasance da yaron, yayinda yake girma. Ya yi zama a jeji, ya kuma zama maharbi. |
and he settled in the wilderness of Paran. His mother arranged for him to marry a woman from the land of Egypt. | Yayinda yake zama a Jejin Faran, sai mahaifiyarsa ta samo masa mata daga Masar. |
About this time, Abimelech came with Phicol, his army commander, to visit Abraham. “God is obviously with you, helping you in everything you do,” Abimelech said. | A lokacin nan Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka zo suka ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai a ko mene ne kake yi. |
“Swear to me in God’s name that you will never deceive me, my children, or any of my descendants. I have been loyal to you, so now swear that you will be loyal to me and to this country where you are living as a foreigner.” | Yanzu ka rantse mini a nan a gaban Allah cewa, ba za ka yaudare ni ko ’ya’yana ko kuma zuriyata ba. Ka nuna mini alheri, kai da ƙasar da kake zama baƙunci kamar yadda na nuna maka.” |
Abraham replied, “Yes, I swear to it!” | Ibrahim ya ce, “Na rantse.” |
Then Abraham complained to Abimelech about a well that Abimelech’s servants had taken by force from Abraham’s servants. | Sa’an nan Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek game da rijiyar ruwan da bayin Abimelek suka ƙwace. |
“This is the first I’ve heard of it,” Abimelech answered. “I have no idea who is responsible. You have never complained about this before.” | Sai Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan ba. Ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba, sai yau.” |
Abraham then gave some of his sheep, goats, and cattle to Abimelech, and they made a treaty. | Sai Ibrahim ya kawo tumaki da shanu ya ba wa Abimelek, sai su biyun suka yi yarjejjeniya. |
But Abraham also took seven additional female lambs and set them off by themselves. | Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke, |
Abimelech asked, “Why have you set these seven apart from the others?” | sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?” |
Abraham replied, “Please accept these seven lambs to show your agreement that I dug this well.” | Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.” |
Then he named the place Beersheba (which means “well of the oath”), because that was where they had sworn the oath. | Saboda haka aka kira wurin Beyersheba, domin a nan ne su biyun suka yi rantsuwa. |
After making their covenant at Beersheba, Abimelech left with Phicol, the commander of his army, and they returned home to the land of the Philistines. | Bayan da aka yi yarjejjeniya a Beyersheba, sai Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka koma ƙasar Filistiyawa. |
Then Abraham planted a tamarisk tree at Beersheba, and there he worshiped the Lord , the Eternal God. | Sai Ibrahim ya shuka itacen tsamiya a Beyersheba, a can kuma ya kira bisa sunan Ubangiji , Allah Madawwami. |
And Abraham lived as a foreigner in Philistine country for a long time. | Ibrahim kuwa ya zauna a ƙasar Filistiyawa na dogon lokaci. |
Some time later, God tested Abraham’s faith. “Abraham!” God called. “Yes,” he replied. “Here I am.” | Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.” |
“Take your son, your only son—yes, Isaac, whom you love so much—and go to the land of Moriah. Go and sacrifice him as a burnt offering on one of the mountains, which I will show you.” | Sai Allah ya ce, “Ka ɗauki ɗanka, makaɗaicin ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi yankin Moriya, ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a can a kan ɗaya daga cikin duwatsun da zan nuna maka.” |
The next morning Abraham got up early. He saddled his donkey and took two of his servants with him, along with his son, Isaac. Then he chopped wood for a fire for a burnt offering and set out for the place God had told him about. | Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa. |
On the third day of their journey, Abraham looked up and saw the place in the distance. | A rana ta uku Ibrahim ya ɗaga ido sai ya ga wurin daga nesa. |
“Stay here with the donkey,” Abraham told the servants. “The boy and I will travel a little farther. We will worship there, and then we will come right back.” | Ibrahim ya ce wa bayinsa, “Ku tsaya a nan da jakin, ni da yaron kuwa mu haura can. Za mu yi sujada sa’an nan mu komo wurinku.” |
So Abraham placed the wood for the burnt offering on Isaac’s shoulders, while he himself carried the fire and the knife. As the two of them walked on together, | Ibrahim ya ɗauki itace saboda hadaya ta ƙonawa ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuwa ya riƙe wuƙa da wutar. Yayinda su biyun suke tafiya, |
Isaac turned to Abraham and said, “Father?” “Yes, my son?” Abraham replied. “We have the fire and the wood,” the boy said, “but where is the sheep for the burnt offering?” | sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?” Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!” Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?” |
“God will provide a sheep for the burnt offering, my son,” Abraham answered. And they both walked on together. | Ibrahim ya amsa ya ce, “Ɗana, Allah kansa zai tanada ɗan ragon hadayar ƙonawa.” Sai su biyu suka ci gaba da tafiya. |
When they arrived at the place where God had told him to go, Abraham built an altar and arranged the wood on it. Then he tied his son, Isaac, and laid him on the altar on top of the wood. | Sa’ad da suka isa wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya kuma shisshirya itacen a kai. Ya ɗaura ɗansa Ishaku, ya kwantar da shi a kan itacen, a bisa bagaden. |
And Abraham picked up the knife to kill his son as a sacrifice. | Sa’an nan Ibrahim ya miƙa hannunsa ya ɗauki wuƙar don yă yanka ɗansa. |
At that moment the angel of the Lord called to him from heaven, “Abraham! Abraham!” “Yes,” Abraham replied. “Here I am!” | Amma mala’ikan Ubangiji ya kira shi daga sama ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!” Sai Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.” |
“Don’t lay a hand on the boy!” the angel said. “Do not hurt him in any way, for now I know that you truly fear God. You have not withheld from me even your son, your only son.” | Mala’ikan ya ce, “Kada ka yi wa yaron nan rauni. Kada kuma ka ji masa ciwo. Yanzu na san cewa kana tsoron Allah, gama ba ka hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba.” |
Then Abraham looked up and saw a ram caught by its horns in a thicket. So he took the ram and sacrificed it as a burnt offering in place of his son. | Ibrahim ya ɗaga ido, ya duba, sai ya ga rago da ƙahoninsa a kafe a wani ɗan kurmi. Sai Ibrahim ya tafi ya kamo ragon ya miƙa shi hadaya ta ƙonawa a maimakon ɗansa. |
Abraham named the place Yahweh-Yireh (which means “the Lord will provide”). To this day, people still use that name as a proverb: “On the mountain of the Lord it will be provided.” | Ibrahim kuwa ya ba wa wurin suna, Ubangiji Zai Tanada. Gama kamar yadda ake ce har yă zuwa yau, “A bisan dutsen Ubangiji , za a tanada.” |
Then the angel of the Lord called again to Abraham from heaven. | Mala’ikan Ubangiji ya kira Ibrahim daga sama sau na biyu |
“This is what the Lord says: Because you have obeyed me and have not withheld even your son, your only son, I swear by my own name that | ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji , domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba, |
I will certainly bless you. I will multiply your descendants beyond number, like the stars in the sky and the sand on the seashore. Your descendants will conquer the cities of their enemies. | tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu, |
And through your descendants all the nations of the earth will be blessed—all because you have obeyed me.” | ta wurin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka, domin ka yi mini biyayya.” |
Then they returned to the servants and traveled back to Beersheba, where Abraham continued to live. | Sa’an nan Ibrahim ya koma wurin bayinsa, suka kuma kama hanya tare zuwa Beyersheba. Ibrahim kuwa ya yi zamansa a Beyersheba. |
Soon after this, Abraham heard that Milcah, his brother Nahor’s wife, had borne Nahor eight sons. | Bayan wani ɗan lokaci, sai aka faɗa wa Ibrahim cewa, “Ga shi, Milka ita ma ta haifa wa Nahor ɗan’uwanka, ’ya’ya maza; |
The oldest was named Uz, the next oldest was Buz, followed by Kemuel (the ancestor of the Arameans), | ɗan fari shi ne Uz, ɗan’uwansa kuma Buz, Kemuwel (shi ne mahaifin Aram), |
Kesed, Hazo, Pildash, Jidlaph, and Bethuel. | Kesed, Hazo, Fildash; Yidlaf, da kuma Betuwel.” |
(Bethuel became the father of Rebekah.) In addition to these eight sons from Milcah, | Betuwel ya haifi Rebeka. Milka ta haifa wa Nahor ɗan’uwan Ibrahim waɗannan ’ya’ya maza takwas. |
Nahor had four other children from his concubine Reumah. Their names were Tebah, Gaham, Tahash, and Maacah. | Ban da haka ma, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifa masa ’ya’ya maza, Teba, Gaham, Tahash da kuma Ma’aka. |
When Sarah was 127 years old, | Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya. |
she died at Kiriath-arba (now called Hebron) in the land of Canaan. There Abraham mourned and wept for her. | Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita. |
Then, leaving her body, he said to the Hittite elders, | Sai Ibrahim ya tashi daga gefen matarsa da ta mutu, ya yi magana da Hittiyawa. Ya ce, |
“Here I am, a stranger and a foreigner among you. Please sell me a piece of land so I can give my wife a proper burial.” | “Ni baƙo ne, kuma baƙo a cikinku. Ku sayar mini da wani wuri yă zama wurin binnewa a nan, domin in binne mataccena.” |
The Hittites replied to Abraham, | Hittiyawa suka ce wa Ibrahim, |
“Listen, my lord, you are an honored prince among us. Choose the finest of our tombs and bury her there. No one here will refuse to help you in this way.” | “Ranka yă daɗe, ka saurare mu. Kai babban yerima ne a cikinmu. Ka binne mataccenka a kabari mafi kyau na kaburburanmu. Babu waninmu da zai hana ka kabarinsa don binne mataccenka.” |
Then Abraham bowed low before the Hittites | Sai Ibrahim ya tashi ya rusuna a gaban mutanen ƙasar, wato, Hittiyawan. |
and said, “Since you are willing to help me in this way, be so kind as to ask Ephron son of Zohar | Ya ce musu, “In kuna so in binne mataccena, sai ku ji ni, ku roƙi Efron ɗan Zohar a madadina |
to let me buy his cave at Machpelah, down at the end of his field. I will pay the full price in the presence of witnesses, so I will have a permanent burial place for my family.” | domin yă sayar mini da kogon Makfela, wanda yake nasa, wannan da yake a ƙarshen filinsa. Ku ce masa yă sayar mini a cikakken farashi, yă zama mallakata domin makabarta tsakaninku.” |
Ephron was sitting there among the others, and he answered Abraham as the others listened, speaking publicly before all the Hittite elders of the town. | Efron mutumin Hitti yana zaune a cikin mutanensa, sai ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birni. |
“No, my lord,” he said to Abraham, “please listen to me. I will give you the field and the cave. Here in the presence of my people, I give it to you. Go and bury your dead.” | Ya ce, “A’a, ranka yă daɗe, ka ji ni, na ba ka filin, na kuma ba ka kogon da yake cikinsa. Na ba ka shi a gaban mutanena. Ka binne mataccenka.” |
Abraham again bowed low before the citizens of the land, | Ibrahim ya sāke rusuna a gaban mutanen ƙasar |
and he replied to Ephron as everyone listened. “No, listen to me. I will buy it from you. Let me pay the full price for the field so I can bury my dead there.” | ya ce wa Efron a kunnuwansu, “Ka ji, in ka yarda. Zan biya farashin filin. Ka karɓa daga gare ni don in iya binne mataccena a can.” |
Ephron answered Abraham, | Efron ya ce wa Ibrahim, |
“My lord, please listen to me. The land is worth 400 pieces of silver, but what is that between friends? Go ahead and bury your dead.” | “Ka saurare ni, ranka yă daɗe; darajan filin ya kai shekel ɗari huɗu na azurfa, amma mene ne wannan a tsakanina da kai? Ka binne mataccenka.” |
So Abraham agreed to Ephron’s price and paid the amount he had suggested—400 pieces of silver, weighed according to the market standard. The Hittite elders witnessed the transaction. | Ibrahim ya yarda da sharuɗan Efron, sai ya auna masa farashin da ya faɗa a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu na azurfa, bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi a lokacin. |
So Abraham bought the plot of land belonging to Ephron at Machpelah, near Mamre. This included the field itself, the cave that was in it, and all the surrounding trees. | Ta haka filin Efron a Makfela kusa da Mamre, wato, filin da kogon a cikinsa, da kuma dukan itatuwan da suke cikin iyakoki filin, aka |
It was transferred to Abraham as his permanent possession in the presence of the Hittite elders at the city gate. | ba wa Ibrahim a matsayin mallakarsa a gaban dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birnin. |
Then Abraham buried his wife, Sarah, there in Canaan, in the cave of Machpelah, near Mamre (also called Hebron). | Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana. |
So the field and the cave were transferred from the Hittites to Abraham for use as a permanent burial place. | Da filin da kuma kogon da yake cikinsa, Hittiyawa suka tabbatar wa Ibrahim a matsayin makabarta. |
Abraham was now a very old man, and the Lord had blessed him in every way. | Yanzu fa Ibrahim ya tsufa, yana da shekaru masu yawa, Ubangiji kuma ya albarkace shi a kowace hanya. |
One day Abraham said to his oldest servant, the man in charge of his household, “Take an oath by putting your hand under my thigh. | Sai Ibrahim ya ce wa babban bawan gidansa, wanda yake lura da duk abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata. |
Swear by the Lord , the God of heaven and earth, that you will not allow my son to marry one of these local Canaanite women. | Ina so ka rantse da sunan Ubangiji Allah na sama da ƙasa, cewa ba za ka samo wa ɗana mata daga ’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama cikinsu ba. |
Go instead to my homeland, to my relatives, and find a wife there for my son Isaac.” | Amma za ka tafi ƙasata da kuma cikin ’yan’uwana, ka samo mata saboda ɗana Ishaku.” |
The servant asked, “But what if I can’t find a young woman who is willing to travel so far from home? Should I then take Isaac there to live among your relatives in the land you came from?” | Bawan ya ce masa, “Me zai faru in matar ba tă yarda tă zo tare da ni zuwa wannan ƙasa ba? In komar da ɗanka a ƙasar da ka fito ne ke nan?” |
“No!” Abraham responded. “Be careful never to take my son there. | Ibrahim ya ce, “Ka tabbata ba ka komar da ɗana can ba.” |
For the Lord , the God of heaven, who took me from my father’s house and my native land, solemnly promised to give this land to my descendants. He will send his angel ahead of you, and he will see to it that you find a wife there for my son. | Ubangiji Allah na sama, wanda ya fitar da ni daga gidan mahaifina, da kuma ƙasar asalina wanda kuma ya yi magana da ni, ya yi mini alkawari da rantsuwa cewa, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa, zai aika mala’ikansa yă sha gabanka domin ka samo wa ɗana mata daga can. |
If she is unwilling to come back with you, then you are free from this oath of mine. But under no circumstances are you to take my son there.” | In matar ba tă yarda tă zo tare da kai ba, za a kuɓutar da kai daga wannan rantsuwa. Sai dai kada ka kai ɗana a can.” |
So the servant took an oath by putting his hand under the thigh of his master, Abraham. He swore to follow Abraham’s instructions. | Saboda haka bawan ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar maigidansa Ibrahim, ya kuma rantse masa game da wannan al’amari. |